GWAMNATIN JIHAR KANO TA AMINCE AYI SALLAR IDI

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa za’a gabatar da  Idin karamar Sallah a daukacin masallatan jihar Kano baki daya tare da bin duka wasu ka’idoji domin kaucewa kamuwa da cutar  covid 19.

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya amince da gabatar da Sallar sannan kuma ya sake amincewa da yin ibadu ga mabiya addinin Kirista a ranar Lahadi suma bisa bin duk wasu tsare tsare da aka gindaya.

Da yake mayar da martani game da kalaman gwamnatin tarayya na cewa kada a gudanar da duk wasu al’amuran da suka shafi addinai Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, yace suna aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya wajen dakile bazuwar cutar Corona.

Sannan yace gwamnatin jihar Kano na ganawa da jagororin tsaron jihar Kano kan yadda za’a gabatar da aikin.