Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya amince da sallamar Engr. Mu’azu Magaji Dansarauniya daga mukaminsa na shugaban kwamitin bunkasa masana antu da kula da aikin shimfida bututun mai na Kamfanin NNPC da iskar Gas ta AKK, wanda sallamar ta fara aiki nan take.
An sanar da cewa an dauki wannan mataki na tsige shugaban kwamitin ne sakamakon shantakewa da rashin tabuka ani abun azo a gani kan nauyin da aka dora masa na kula da aikin.
A wata sanarwa dauke da sa hannu kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba, yace an nada Engr. Magaji tun a watan Aprilu shekarar bara domin ya shugabanci kwamitin bisa fatan da ake da shi na ganin ya kula da aikin yadda ya kamata wanda bisa mamaki ya gaza tabuka wani abun azo a gani a aikin.
A karshe gwamnan ya gode masa tare da yi masa fatan alkhairi da samun cikakkiyar nasara a rayuwa.