Gwamnatin Jihar Jigawa Za Ta Raba Kayan Abinci Ga Al’umma A Cikin Watan Azumin Ramadan

Gwamnatin jihar Jigawa ta sahale a rarraba kayan abinci da suka hada da buhun shinkafa dubu 27 da kuma kwalayen taliya dubu 10 da dari 800 ga al’umma a cikin watan azumin Ramadan.

Kwamishinan yada labarai, wanda ke a matsayin na matasa, wasanni da kuma al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, inda yace gwamnatin jihar ta dauki matakin ne bayan da majalisar zartarwa ta jihar ta gudanar da taron ta a makon da muke ciki.

Kazalika yace majalisar ta karbi rahoto daga ma’aikatar ayyuka na musamman inda ta bayar da kwangilar raba hatsi ga al’ummar jihar a lokacin azumin, a wani yunkuri na tallafin rage radadi da ake fuskanta.

Leave a Reply