Gwamnatin Jihar Borno tace adadin ‘yan kungiyar boko haram basu da yawa a yanzu

Gwamnatin Borno tace kashi 95 cikin 100 na ‘Yan Boko Haram na mutuwa da Akidar ta

Gwamnatin jihar Borno tace sama da kashi 95 cikin 100 na mutane masu akidar kungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram, musamman wadanda suka kafa kungiyar na mutuwa ne da akidar ta a zukatansu ko kuma su mika wuya.

Mashawarci na musamman ga gwamnatin jihar Borno kan lamuran tsaro, Birgediya Janaral Ishaq Abdullahi mai ritaya, shine ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi a Birnin Maiduguri.

Yace manyan jiga-jigan kungiyar tuni sun jima da mutuwa ta rushe, wanda a yanzu baifi mutum 10 a ‘ya’yan kungiyar da wata kila suke a raye ba.

Abdullahi yace da yawa daga cikin manyan kwamandojin kungiyar sun mutu saboda gumurzu kan shugabanci, tsakanin Mayakan kungiyar ISWAP da na Boko Haram, masu biyayya ga tsagin Marigayi Abubakar Shekau bayan mutuwar sa a shekarar 2021.

Daga: Idris Usman Alhassan Rijiyar Lemo, Murtala Shehu Abubakar

Leave a Reply