Gwamnati ta yi asarar naira miliyan 113 saboda dakatar da jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya ta ce gwamantin tarayya ta yi asarar kuɗi kimanin naira miliyan 113 sakamakon dakatar da jirgin ƙasan Abuja zuwa ƙaduna na tsowan watanni takwas.

Babban daraktan hukumar Fidet Okhiria ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran ƙasa NAN.

Ya ƙara da cewa wasu ma da yawa daga cikin ɗaiɗaikun ‘yan ƙasar asarar ta shafe su sakamakon tsaida zirga-zirgar jirgin inda ya bayyana cewa Akwai mutanen da ke gudanar da sana’o’i daban-daban a tasoshin jiragen, kuma  suna samun ciniki.

Leave a Reply