Gwamnan Kano ya amince da naɗin sabon shugabancin tashar talabijin ta ART

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Hajiya Hauwa Ibrahim, a matsayin mai riƙon shugabancin tashar talabijin ta jihar, wato Abubakar Rimi Television.
Naɗin ya biyo bayan dakatar da Mustapha Indabawa a matsayin manajan darekta na tashar.
Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi ne ya fitar da takardar naɗin, inda a cikin wasiƙar ya umarci Hajiya Hauwa Ibrahim ta karɓi ragamar jagorancin tashar, nan take.
Kafin naɗin na yanzu Hajiya Hauwa, ita ce mataimakiyar manajan darektan tashar talabijin ɗin.
Idan ba a manta ba gwamnatin jihar ta Kano ta shigar da tuhuma bakwai a gaban hukumar yaƙi da rashawa ta jihar, kan shugaban da aka dakatar, da kuma babban jami’in ma’aikata na tashar Ibrahim M. Bello – tuhumar da ta ƙunshi aikata mugun laifi da ɓarna da kuma karkatar da kuɗaɗe.

Leave a Reply