Gwamnan Jihar Lagos ya rage kudin sufuri da samar da wuraren bayar da taimakon abinci ga talakawa

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ya sanar da kafa wuraren bayar da taimakon abinci ga talakawa da sauran masu rauni a cikin al’umma a sassan jihar sakamakon wahalar da aka shiga a dlilin karancin man fetur da takardar kudin kasar ta naira.

Haka kuma gwamnan ya sanar da rage kudin hawa motoci da sauran abubuwan sufuri na haya na gwamnatin jihar da kashi hamsin cikin dari daga yau din nan.

Gwamnan jihar ta Lagos ya kuma bayar da umarni na gaggawa ga dukkanin gidajen mai da ke jihar da su rika sayar da mai ba dare da rana tsawon sa’a domin masu ababen hawa su daina tsayuwa sayen mai tsawon sa’o’i.

A sanarwar da ya fitar ya gargadi bata-gari da sauran miyagu wadanda za su nemi ribatar tsarinwajen haddasa rikici, da cewa duk wanda ya yi kokarin hakan zai gamu da hukunci.

Sanwo-Olu ya bayyana cewa kalubalen da ke tattare da sauyin kudin ya haddasa matsala ga mazauna birnin na Lagos, inda suka shiga matsi da ya takaita hanyoyin samun kudin da suke hada-hada a kullum wanda hakan ya kuma jefa su cikin wahala.

Leave a Reply