Gwamnan jihar Katsina Dr Dikko Radda, ya ce a cikin shekara guda gwamnatinsa ta samu nasarar rage ayyukan ta’addanci da kashi 70.

A cewarsa nasarar hakan ta samune bisa hadin gwiwar da aka samu tsakanin jami’an tsaro da kuma wanda jihar ta kirkira.
Ya ce abinda ‘yan bindiga ke yi a yanzu bai wuce abinda masu iya magana kan kira da shure-shure ba, na kokarin nuna cewar har yanzu suna da karfinsu.
Gwamna Radda dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin Yola babban birnin jihar Adamawa.
Ya ce lokaci ya yi da ya kamata ace an samar da ‘yan sandan jihohi a kasar don yaki da ayyukan ta’addanci, inda ma ya bada misali da yadda ake da irinsu a kasashen da suka ci gaba don inganta tsaron rayuka da dukiyar jama’a.

Leave a Reply