Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf Yace Kwamitocin Bincike Biyu Da Gwamnatinsa Ta Kafa Ba Wai An Kafasu Ne Domin Farautar Wani Ba

Majalisar Kasa Ta Bayyana Dalilan Watsi Da Zarge-zargen Badakalar Naira Biliyan 178 A Kan Shugaban NPA

Majalisar Wakilai ta bayyana dalilan da suka sa ta wanke Shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya NPA, Alhaji Mohammed Bello Koko daga zarge-zargen badaqalar bashin naira biliyan 178 da ke tattare a rahoton yadda hukumar ta gudanar da ayyukanta na shekarar 2019.

Shugaban kwamitin majalisar wakilai da ke sauraron korafe-korafe, Hon Mike Etaba, ya bayyana mastayar majalisar a zaman bayyanar jama’a da aka yi aAbuja a makon da ya gabata.

Idan za a iya tunawa wata kungiya mai zaman kantamai suna ‘Forum of Nongovernmental Organisations in Nigeria’ ta zargi NPA da Bello-Koko a kan badakalar naira biliyan 178 na kudaden da suka makale daga basukan da hukumar take bi wadanda ke tatteare a cikin rahotonin hukumar na shekarar 2019.

LD

Gwamnan jahar kano Abba kabir Yusuf ya bayyana cewa kwamitocin bincike guda biyu da gwamnatinsa ta kafa ba an kafa su bane domin farautar wani ba

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a yayin da ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Kano,Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ya kai ziyarar ban girma gidan gwamnatin jahar kano a wani bangare na Hawan Nassarawa daya gudana a jiya juma’a

Gwamna abba kabir yusuf ya kuma bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a gwamnati da kuma magance matsalar tashe-tashen hankulan siyasa a jihar.

Inda Ya sha alwashin yin bincike tare da kamo wadanda suka tayar da tarzomar siyasa , yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta kyale kowa ba, ba tare da laakari da jamiyyun siyasarsu ba.
DT/MJB

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani, ya ce sama da makarantu 1,500; a kananan hukumomi takwas na jihar ba su da katangu

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani, ya ce sama da makarantu 1,500; a kananan hukumomi takwas na jihar ba su da katangu .
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 23 na jihar.

Gwamnan, ya bayyana cewa a wani bangare na kudirin gwamnatinsa na aiwatar da shirin Safe School Initiative, fitattun yan kasuwar jahar , Alhaji Adamu Atta da kuma Alhaji Bukar Shettima,sun shirya gina katangu ga makarantu 100.

Yana mai bayyana cewa gwamnatinsa na mai da hankali kan ilimi duba da cewa ilimi na daya daga cikin abinda ya kamata a baiwa fifiko DT/MJB

NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutum daya tare da tabbatar da samu bullar cutar zazzabin Lassa
Daga bangaren lafiya kuma , hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutum daya tare da tabbatar da samu bullar cutar zazzabin Lassa guda 15 cikin mako guda a fadin kasar.

Hukumar NCDC ta bayyana haka ne a wani rahoto na mako 13 da aka buga a shafinta na yanar gizo ranar Juma’a.

Hukumar NCDC ta ce an samu raguwar adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar daga mutum 25 a mako na 12 zuwa na 15 a cikin makon da ya gabata, yayin da adadin wadanda ake zargi sun kamu da cutar ya karu idan aka kwatanta da na shekarar 2023.

Idan aka tattara daga mako na daya zuwa na 13, kasar ta sami rahoton mutane 806 da aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma mutuwar mutane 150, yayin da da adadin wadanda suka mutu ya kai kashi 18.6 cikin dari, sama da adadin wadanda suka mutu a shekarar 2023.
PNC/MJB

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa Gwamna Inuwa Yahaya, ya bayyana matukar alhininsa game da rasuwar Gwamnan farar hula na farko a Abia kuma tsohon ministan kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, Ogbonnaya Onu.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yadda labarai na jahar Gombe Ismaila Uba-Misilli ya fitar .

a sakon ta’aziyyar tasa a madadin gwamnonin Arewa 19, ya bayyana cewa marigayi Onu ya bayar da gagarumar gudunmawa a fagen siyasar Najeriya.

NAN

Leave a Reply