Gwamnan jihar  Imo yace ‘yan siyasa ne masu hannu a matsalar tsaron Najeriya

A wani makamancin labarin kuwa; Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya ce harin da aka kai babban ofishin INEC da ke Owerri ya nuna cewa akwai hannun ‘yan siyasa a matsalar tsaron da ke addabar jihar.

Da yake jawabi ga manema labarai a shalkwatar ‘yan sanda a yau, gwamnan ya ce masu tsatsauran ra’ayi ne suka kai harin.

Gwamnan ya kara da cewa yana jin dadin aikin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro, kuma zasu ci gaba da basu goyon baya. Uzodinma ya yi alkawarin cewa lamuran tsaro za su inganta a jihar,  kafin bukukuwan kirismeti

Leave a Reply