Gwamnan Jigawa, ya nuna damuwarsa kan yadda gwamnati ta biya ASUU rabin albashi.

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, ya nuna damuwarsa kan yadda gwamnatin tarayya ta biya kungiyar ASUU rabin albashi da hakan ya maida hannun agogo-baya ta fuskar ilmi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin taron kaddamar da sabbin shugabannin kungiyar dalibai ta kasa a Abuja, inda ya ce gwamnatinsa zata ci gaba da bawa dalibai gudummuwar da ta dace.

Ya ce shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya damu matuka kan halin da daliban kasar nan suke ciki sakamakon yajin  aikin kungiyar ASUU, tare da shan alwashin hana afkuwar hakan anan gaba. A nashi jawabin, shugaban kungiyar daliban ta kasa Comrade Usman Barambu, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba batun muradun malaman kasar nan domin kawo karshen dambarwar dake tsakanin bangarorin biyu.

Leave a Reply