GWAMNA ZULUM YAKAI ZIYARAR BAZATA KANANAN HUKUMOMIN JIHAR BORNO

Rahotanni sun bayyana cewa Dayawa daga cikin manyan jami’an gwamnati na kananan hukumomin jihar Borno 6 basa wuraren aikin su a lokacin Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum yakai ziyarar bazata zuwa ga shalkawatar mulkin kananan hukumomin.

Daga cikin kananan hukumomin da gwamnan ya halarta sun hadar da karamar hukumar Chibok da Konduga da Bama da dai sauran su.

Mai Magana da yawun gwamna Zulum Malam Isa Gusau ne ya bayyana haka inda yace yayin da gwamnan yakai ziyarar bazatan domin duba wasu ayyuka dayawa daga cikin manyan jami’an basu halarci wuraren aikin su ba.

Yace kazalika Gwamnan ya samu ganawa da shugabannin gargajiya na kananan hukumomin Bama Askira Gwoza a fadar mulkin su.