Gwamna Zulum ya bada umarnin hada cibiyoyin koya sana’o’i a makarantun Tsangaya.
Gwamna Babagana Umar Zullum na Jihar Borno ya umarci hukumar gudanarwar kula da ilimin makarantun islamiyya da tsangayu data samar da cibiyoyin koya sana’o’i a makarantun koyon ilimin Qur’ani guda 451 dake fadin jihar.
Zulum ya bayar da umarnin ne yayin da shugaban hukumar Khalifa-Ali Abdulfathi yake gabatar masa da rohoto kan makarantun ‘’Tsangaya’’.

Gwamnan ya kuma jadadda kudirin gwamnatin jihar na daidaita harkar ilimin yau da kullum a tsarin bayar da ilimin jihar.