Gwamna Zulum na jihar Borno ya bayar da umurnin kama ƴan bangan siyasa

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana takaicinsa kan yawan tashin hankulan da ake samu tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa a jihar.

A wata sanarwa da ta fito ta hannun mai taimaka wa gwamnan kan kafafen yaɗa labarai, Isa Gusau, ta ce an fi samun rikicin ne tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da kuma na PDP mai hamayya.

Gwamnan ya buƙaci kwamishinan ƴan sanda na jihar da ya gudanar da bincike kan rikice-rikice da aka samu na baya-bayan nan tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk wanda aka samu da laifi gaban kotu don ya fuskanci shari’a

Ya kuma buƙaci ƴan siyasa da masu ruwa da tsaki, da ƴan takara su tabbatar sun gujewa rigingimu a lokutan yaƙin neman zaɓe domin kauce wa shiga hannun hukuma.

Leave a Reply