Gwamna Kano yayi alƙawarin gudanar da bincike ga tsohuwar gwamnatin Ganduje bisa zargin cirar kuɗaɗen yan fansho

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ya yi alƙawarin gudanar da cikakken bincike kan zargin cirar kuɗaɗen garatuti na ‘yan fansho ba bisa ƙa’ida ba a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.
Gwaman ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da kashi na biyu na biyan kuɗin ƴan fansho na garatuti da waɗanda suka mutu wanda ya kai Naira biliyan  5 ga kusan ma’aikata 4,000 da suka yi ritaya.

Gwamna Yusuf ya buƙaci ƙungiyar ’yan fansho ta ƙasa reshen jihar da ta nemi a gudanar da bincike kan kuɗaɗen da suka bata, tare da kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta fara gudanar da cikakken bincike, tare da yin alƙawarin hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen karkatar da kuɗaɗen fansho. 
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da cewa ma’aikatan da suka yi ritaya da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasu sun samu haƙƙoƙinsu.

Leave a Reply