Gwamna Ganduje ya sanya hannu a dokar Masu bukata ta musamma a Kano

Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu a sabuwar dokar masu bukata ta musamman wadda ta bada damar Samar Musu da hukuma a jihar nan.

 Gwamnan ya Sanyawa dokar hannu ne yayin taron majalisar zartarwar ta wanann makon wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar kano.

 Da yake jawabi bayan Sanya hannu a dokar gwamna Ganduje yace an samar da dokar ne domin inganta Rayuwar masu bukata ta musamman, ta hanyar fitar da tsare-tsaren yadda za’a gudanar da aikin inganta Rayuwar su.

Yace Mai bukata ta musamman shi za’a sa a matsayin Shugaban Wannan hukuma, saboda shi yasan halin da yan uwansa suke ciki, Kuma a kunshin Shugabannin hukumar za’a Sanya dukkanin rukunonin Masu bukata ta Musamma dake jihar nan.

 Kafin Sanya hannu aka wannan dokar sai da majalisar dokokin jihar kano tayi aikin ta akai ta kuma amince da ita sannan ta turawa gwamnan Kano domin Sanya hannu akan dokar.

 Yayin Zaman majalisar zartarwar na wannan makon gwamna Ganduje ya Sanyawa dokoki kimanin goma Sha daya hannu bayan amincewa da su.

Leave a Reply