Gwamna Ganduje ya gabatar da N245.3bn a matsayin Kasafin 2023.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya gabatar da kudirin kasafin kudi na Naira biliyan 245.3 ga majalisar dokokin jihar na shekarar 2023.

Kudirin kasafin kudin na shekarar 2023 da aka gabatar yana da biliyan N144.6 a matsayin na manyan ayyuka  wanda ke wakiltar kashi 59 cikin 100 na jimillar kasafin kudin, yayin da kudaden da ake kashewa na yau da kullum a cikin kudirin da aka gabatar ya tasamma sama da biliyan 100, wanda ke wakiltar kashi 41 cikin 100 na kasafin.

Wakilinmu Yusuf Idris Gama, ya rawaito mana cewa wannna shi ne kasafin kudi  na karshe da Ganduje ya gabatar a gaban majalisar dokokin jihar domin a watan Mayun shekara mai zuwa ne ake sa ran zai kammala wa’adin mulkinsa.

A shekarar da ta gabata Gwamna Abdullahi Ganduje ya gabatar da sama da Naira Biliyan dari da casa’in da shida N196 ga majalisar dokokin Jihar Kano, na shekarar 2022.

Leave a Reply