Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River ya sayawa jami’an sojin ruwan kasar nan wasu nau’ikan jiragen ruwa domin yakar matsalar tsaron dake kara kamari hadi da kakkabe aiyukan ‘yan fashin teku da masu fasa bututun mai a yankin Calabar da garuruwan da ruwa ya ratsa ta cikin su a jihar.
Babban daraktan kula da yadda aiyukan da suka shafi hanyoyin ruwa ke tafiya a jihar Mista Bobby E. Ekpenyong, wanda ya tabbatar da hakan lokacin da ya karbi kiran waya daga Shugaban karamar hukumar Bakassi Mista Iyadim Amboni Iyadim, yace nan bada jimawa za’a mika jiragen ga jami’an tsaron jihar masu taken aiki da kwarewa.
Mista Ekpenyong yace tabarbarewar tsaron da aka sanar da gwamnan cewa ta addabi hanyoyin ruwan ita tasa daukar matakin samar da jiragen da be bayyana adadadin yawansu.
Da yake maida jawabi Shugaban karamar hukumar Bakassi Mista Iyadim Amboni Iyadim yace,matakin da gwamnan ya dauka na siyo jiragen ruwan abune da yadace, domin kuwa zai habaka tattalin arzqin yankin na bakasi da kawo karshen matsalar a jihar Baki daya.