Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya gabatar da kasafin kudi na shekarar 2023 gaban zauren majalisar dokokin jihar

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya gabatar da Daftarin kasafin kudi na naira biliyan 202 gaban zauren majalisar dokokin jihar.

Yayin gabatar da kasafin Bala Muhammad ya bayyanawa zauren majalisar kudirin gwamnatinsa na ganin ta kammala daukacin aikace aikacen da ake cigaba da aiwatarwa a fadin jihar, kafin karewar wa’adinsa na farko a shekara ta 2023, yana mai bayyana cewa an samu karin sama da kashi 2 a kasafin idan aka kwatanta da shekarar data gabata.

Da yake mayar da jawabi, Shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Y Suleiman yace za su kokari wajen gaggauta amincewa Daftarin kasafin kudin da aka gabatar musu kafin karshen shekarar nan don tabbatar da ganin an fara aiki dashi a shekara ta 2023.

Leave a Reply