Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya sanya dokar haramta amfani da babura a yankin Mbamba, Yolde Pate da karamar hukumar Yola ta kudu.
Ya kuma sanya dokar amfani da su a yankin Viniklang da rukunin gidajen gwamnatin tarayya dake yankin karamar hukumar Girei daga karfe 5 na yamma zuwa 5 na Safiya.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Humwashi Wonosikou, ya rabawa manaima labarai.
Gwamnatin jihar tace ba’ayi hakan domin a kuntatawa jama’a ba sai dan a kawo karshen matsalolin masu aikata miyagun laifuka da wanzar da zaman lafiya a jihar.