Gini ya rufta kan wasu mutane a Kenya

Masu aikin ceto na neman akalla mutum goma, mafi yawansu masu aikin gini, waɗanda ake fargabar sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan wani gini da ya faɗi a birnin Nairobi na ƙasar Kenya.

Ana cikin aikin ginin – mai hawa bakwai – a lokacin da ya faɗi ranar Talata da rana a yankin Kasarani da ke wajen birnin.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa sau biyu hukumomin na gargaɗi ga mai kula da ginin da ya dakatar da ginin saboda rashin tsari da ingancin ginin.

Faɗuwar gine-ginen da ba a kammala ba abu ne da ya zama ruwan dare a ƙasar.

Masu aikin ceto na ci gaba da aiki domin zaƙulo mutanen da suka akale a cikin ɓaraguzan ginin.

Leave a Reply