Gimbiyar Sussex, Meghan ta ce kaso 43% na kwayoyin halittunta na da alaka da Najeriya.

Gimbiyar Sussex, Meghan Markel, ta bayyana cewa bayan gwajin kwayoyin halittu na DNA da ta gudanar kan gane asalinta da salsalar zuri’arsu ta gano cewa kaso 43 na da alaka da Najeriya.

Gimbiyar ta dauki wannan mataki ne a yayin cigaba da daukar fim din ta mai dogon zango mai suna “Archetypes.”

A shirin wannan makon an maida hankali ne kan dambarwar dake tattare da wata jaruma bakar fata da ta fuskanci kalubale daga turawa.

A yayin tattaunawa da wasu jaruman da suka taka rawa a shirin Gimbiya Meghan, ta tattauna da su kan sakamakon asalinta inda suka yi ta raha cikin nishadi tare da bakin na ta da suka hadar da  Issa Rae, Emily Bernard, da  Ziwe Fumodoh.

Gimbiya Meghan dai na auren Yarima Harry na masarautar Burtaniya.

Leave a Reply