Gerard Pique na Barcelona zai yi ritaya daga Tamaula.

Dan wasan bayan Barcelona Gerard Pique yace ya shirya tsaf domin yin ritaya daga kwallon kafa a wasan karshen da zai bug ana karshe a filin wasan na Nou Camp a ranar Asabar.

Dan wasan mai shekara 35, wanda ya taso a kungiyar ta Barcelona ya shafe shekara hudu a Manchester United, ya yi wannan sanarwar a wani biiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Barcelona za ta yi wasa da Almeria a La Liga ranar Asabar wanda zai zama wasan karshe ga Pique.

Leave a Reply