Garin da ake ɗaukar marasa lafiya a makara zuwa asibiti a Yobe

  • Haruna Kakangi
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,Jounalist
  • Twitter,@@kakangi01
  • Aiko rahoto dagaAbuja
  • Tushe@bbchausa.com

Tafiyar kilomita 27 ne tsakanin ƙauyen da ake kira Illela da asibiti mafi kusa a garin Gashua na jihar Yobe, da ke arewacin Najeriya.

Amma ba nisan ne babbar matsalar ba, rashin kyawun hanya ne abin da ya fi ci wa al’ummar kauyen tuwo a kwarya.

A lokacin damina Illela kan koma tsibiri, inda ruwa kan zagaye shi, ta yadda ba a iya shiga ko fita sai ta hanyar amfani da kwale-kwale, kuma wannan babban ƙalubale ne musamman a lokacin da aka samu maras lafiya, ciki har da mata masu haihuwa.

A nan ne kauyen da Shafi’u Salisu ke rayuwa tare da matarsa da yara biyu.

Duk da cewa Shafiu ya yi sa’a, yaransa biyu, Zainab da Fatima an haife su ne lokacin rani, dan’uwansa bai yi wannan dacen ba.

Ya ce “lokacin da Hajara, matar yayana za ta haihu, sai muka nemi amalanke muka saka ta a ciki zuwa bakin rafi, daga nan sai muka saka ta a kwale-kwale muka tsallakar da ita kafin muka nemo motar da ta kai ta asibiti.”

Shafi’u ya bayyana haka ne a yayin wata hira da BBC a shirin da muke yi na musamman game da abubuwan da suka shafi rayuwar jama’a gabanin zaɓen Najeriya na 2023.

A shekarar 1999 ne aka gina wa ƙauyen ɗakin shan magani ɗaya tilo da aka taɓa samarwa yankin, to amma tun daga wancan lokacin ɗakin ba ya aiki saboda rashin malaman lafiya.

A yanzu wurin ya lalace, inda ya zamo wurin wasan yara.

Saboda haka a hankalin ƴan’uwa da iyaye ya tashi a lokacin da haihuwar Hajara ta ƙarato, kasancewar lamarin ya zo ne a cikin damina, lokacin ruwa ya yi waƙauyen nasu ƙawanya.

Babu mota ko babur da zai iya shiga ko fita.

“Mata masu ciki ba su cika zuwa awo ba, shi ya sa za ka ga idan aka zo haihuwa ana samun matsala sosai, idan ma za a je asibiti ana fuskantar matsala mai girman gaske,” in ji shi.

“Haka za ka ga an ɗora mai ciki a amalanken shanu zuwa bakin ruwa, daga nan sai a sa ta cikin kwale-kwale a tsallakar da ita, idan a lokacin an yi ruwa, to sai dai a sake ɗaukan ta a amalanke zuwa Garun Dole, inda a can ne za a samu mota ta kai ta Gashua.”

‘Kwalara ta yi mana ɓarna a 2021’

Shafi’u ya ce a shekarar 2021 an yi fama da mumman ciwon amai da gudawa a ƙauyen nasu.

“A wannan lokacin mun zubar da hawaye sosai, kuma abin ya faru ne a lokacin damina, lokacin da ruwa ya zagaye garinmu.”

“Za ka ga an rungumi mutum ko kuma mutum da ransa ka ga an ɗauko shi a cikin makara ko gadon kara, idan aka zo bakin ruwa sai a rasa yadda za a yi saboda kwale-kwalen sun yi kaɗan.”

Ya ƙara da cewa “a lokacin ne na rasa kakana mallam Rabi’u a kan hanyar asibiti, ubangidana ya rasa ƴarsa a kan mashin kafin a kai asibiti sannan akwai maƙwafcina mallam Usman shi ma ƴarsa ƙarama ta rasu kafin a isa asibiti, da dai sauran su.”

 cewarsa kimanin mutane 30 ne suka mutu.

Ya shaida wa BBC cewar tsakanin ƙauyen nasu da gari mafi kusa da za a iya samun asibiti, wato Illela akwai nisan kilomita 27.

“Daga Illela zuwa Garun Dole akwai nisan kilomita 2, sannan daga Garun Dole zuwa Gashua akwai nisan kilomita 25,” in ji shi.

Ya ce kimanin shekara 20 da ta wuce an yi kwalbati wadda take taimaka wa ababen hawa shiga ƙauyen, to amma a tsawon sama da shekara 10 da suka wuce a duk damina ruwan yana shanye hanya, ba a iya ganin kwalbatin, sai dai a yi amfani da kwale-kwale wajen shiga da fita ƙauyen.

Ya ce “kwale-kwalen ma ta kan kwalbatin yake wucewa domin ba ma za ka gane akwai kwalbati a wurin ba.”

‘Ba a yin karatun boko a garinmu’

Wata matsalar ita ce yadda yaran ƙauyen ba su yin karatun boko saboda rashin makaranta.

Shafi’u ya ce “a taƙaice yaran da suke a Illela babu inda suke zuwa makaranta”.

Ya shaida wa BBC cewar tun a 1976 ne aka gina wasu azuzuwa biyu a ƙauyen, waɗanda daga baya iska ta kwashe rufin makarantar kuma aka bar ta ta lalace.Sai dai ya ce a shekara ta 1999 an yi wa makarantar gyara, amma ya ce tun kimanin shekara 10 da suka gabata ne makarantar ta sake lalacewa.

Ya ce “daga ƙarshe yanzu makarantar ta rushe babu inda ɗalibai za su zauna.”

Ya ƙara da cewa yanzu a garin na Illela karatun allo ne kawai yara suke yi.

“Gaskiya ba a karatun zamani a garinmu kwata-kwata, sai dai makarantar allo.”

‘Mun yi ƙorafi har mun gaji’

Hanyar zuwa Illela wadda ababen hawa ba su iya bi idan an yi ruwa

Mallam Shafi’u ya ce manyan matsalolin ƙauyen nasu guda uku ne, wato rashin asibiti, da rashin hanya, da kuma rashin makaranta.

Ya shaida wa BBC cewa sun yi ƙoƙari fiye da sau-shurin-masaƙi wajen isar da koke-kokensu game da matsalolin ga mahukunta, amma babu wani mataki da gwamnati da ɗauka.

Ya ce “dattawanmu suke yin mota ɗaya zuwa mota biyu su je ƙaramar hukumarmu ta Bursari su kai ƙorafi, za kuma a amsa a lokacin amma shiru babu abin da zai faru.”

“Mun tafi, mun tafi, ban san adadin tafiyar mu ba zuwa ƙaramar hukuma domin kai kukanmu kan matsaloli uku da suke addabar mu ba.”

Sai dai ya shaida wa BBC cewar yanzu haka sun saduda, saboda sun gaji da alƙawurran da ba a cikawa daga bakin ƴan siyasa.

A cewarsa akwai cibiyar kaɗa ƙuri’a har guda biyu a ƙauyen saboda yawan al’ummarsa, kuma ƴan siyasa kan ziyarci yankin domin yaƙin neman zaɓe a lokacin siyasa saboda tasirin yawan al’umma.

To amma ya ce ƴan siyasa ba su cika alƙawurran da suke ɗaukar masu.

Leave a Reply