‘Ganduje ba ya cikin gwamnonin da za su biya ma’aikata kuɗi hannu da dukiyar sata’

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rahoton da ke cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na cikin gwamnonin da ke ƙoƙarin halsta kuɗin haram ta hanyar biyan ma’aikata albashi a hannu maimakon ta banki.

Martanin na zuwa ne bayan wata kafar yaɗa labarai ta intanet ta yi iƙirarin cewa hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta saka wa Ganduje ido tare da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da Gwamnan Ribas Nyesom Wike saboda sun ɓoye garin biliyoyin kuɗi a wasu wurare.

Kafin haka, Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya faɗa wa Daily Trust cewa biyu daga cikin gwamnonin sun fito daga arewacin ƙasar nan, yayin da ɗaya ya fito daga kudanci – amma bai faɗi sunayensu ba.

 A cewar sanarwar da Kwamashinan Yaɗa Labarai na jihar  Kano Malam Muhammad Garba ya fitar, duk da cewa EFCC ba ta faɗi sunan gwamnonin ba amma Sahara Reporters ta yi gaban kanta wajen yin iƙirari maras tushe,

Saboda haka ne  aka nemi ta janye labarin tare da neman afuwa, wanda idan ba ta yi haka ba gwamnatin za ta kai ƙara kotu.

Leave a Reply