Gamnatin Buhari ta ce baza ta iya kammala aikin layin doga daga Ribas zuwa Borno ba

Gwamantin Najeriya ta ce ba za ta iya kammala aikin shimfida layin dogo na jirgin ƙasa da ta ce za ta yi da zai hada gabashin ƙasar da kudancin ƙasar ba, kafin ƙarewar wa’adin mulkin shugaban Muhammadu Buhari.

Gwamnatin ta ce kamala aikin shinfada layin dogon ba abu ne mai yiwuwa ba saboda ƙarancin kudaden da za’a yi aikin.

Ministan harkokin sufurin ƙasar Mu’azu Jaji Sambo ne ya sanar da hakan bayan kamala zaman majaslisar zartarwar ƙasar da ya gudana a ranar Laraba.

A cewar sa gwamnatin tarayyar, ba ta sami damar karbar kudin hadin guiwar da za’a gudanar da aikin ba, wanda hakan yasa suka gaza samar da kudaden da suka kamata a yi aikin.

Jihohin da za su ci gajiyar aikin sun haɗa da jihohin Ribas, Abia, Anambra, Imo, Ebonyi da Enugu, da Nasarawa, Benue, Plateau, Kaduna, Yobe, Borno, Bauchi da kuma Gombe.

Shekara biyu da suka gabata ne, tsohon ministan Sufurin Najeriya Rotimi Amaechi, ya ce za a kamala aikin shimfida layin dogon na Fatakwal zuwa Maiduguri kafin karewar mulkin shugaba Buhari.

A lokacin kaddamar da shirin, an kiyasta cewa za a kashe kusan dala biliyan biyu wajen gina layin dogon, wanda suke cewar zai bunƙasa tattalin arzikin jihohin 14 da aikin zai shafa

Leave a Reply