Shugaban Real Madrid Florentino Perez na sa ran ɗan wasan gaban Paris St-Germain da Faransa Kylian Mbappe mai shekara 22 zai koma kulob ɗin a 2022. (El Debate – in Spanish)
Fiorentina ya ce ɗan wasan Serbia mai shekara 21 Dusan Vlahovic wanda ake alaƙantawa da Arsenal da Tottenham bai karɓi wata sabuwar kwantiragi ba da kulob ɗin na Serie A. (Evening Standard).