An dakatar da danwasa Cristiano Ronaldo daga buga wasa guda biyu

Hukumar kwallon kafa ta kasar birtaniya ta dakatar da dan wasan kasar Portugal Cristiano Ronaldo daga buga wasannin na kungiya har guda biyu samunsa da laifin fasa wayar wani yaro magoyin baya da yayi a watan afirilu da ya gabata a wasan da Manchester tayi da kungiyar kwallon kafa ta Everton a shekarar 2022,

an kuma ci tarar Ronaldo mai shekaru 37 £50,000 da kumagargadin kada ya sake yin irin wannan ganganci anan gaba.
Dokar dai zata fara aikine a dukkan wata kungiya da yakoma, sakamakon ya bar kungiyarsa ta Manchester United.

Leave a Reply