Ficewar da ƴan Najeriya ke yi zuwa ƙasashen waje ba laifi ba ne – Adesina

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan yaɗa labarai, Femi Adesina ya ce ba matsala ba ce ficewar da ƙwararru ke yi daga ƙasar  nan zuwa ƙasashen waje domin neman aiki ba.

Adesina ya bayyana haka ne lokacin wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels cikin ƙarshen mako.

Ya ce bai kamata a ɗora wa gwamnatin shugaba Buhari laifin ficewar da da matasan ƙasar ke yi zuwa wasu ƙasashe domin neman aikin yi ba.

A cewar sa matasan na ficewa daga ƙasar nan ne tun kafin zuwan gwamnatin shugaba Buhari.

Masana dai na nuna damuwa kan yadda ƙwararru daga Najeriya, kamar likitoci, da masana kimiyyar yaɗa labarai da sadarwa ke tafiya ƙasashen waje don neman ingantacciyar rayuwa saboda matsi na tattalin arziƙi da ake fama da shi.

Leave a Reply