Fasinja biyu sun mutu bayan motarsu ta afka cikin kogi a Sifaniya

Mutum aƙalla biyu ne suka mutu da tsakar dare bayan motar bas da suke ciki ta afka cikin kogi yayin da suke kan wata gada a yankin Galicia na ƙasar Sifaniya, kamar yadda hukumomin agaji suka bayyana ranar Asabar.

Hatsarin ya faru a daren Juma’a a kusa da Vigo da ke kan iyakar ƙasar da Portugal.

Jaridar La Voz de Galicia ta ruwaito cewa motar na ɗauke da mutanen da suka tafi ziyartar ‘yan uwansu da aka ɗaure a gidan yarin Monterroso da ke tsakiyar Galicia.

Ma’aikatan agaji sun ce an zaƙulo gawar mutum biyu yayin da aka ceto mutum biyu, ciki har da direban motar, kuma aka kai su asibiti.

Leave a Reply