Ethiopia ta cire ƙungiyar TPLF daga jerin ƙungiyoyin ta’addanci

Majalisar dokokin Habasha ta amince da cire sunan ƙungiyar ‘yan tawayen TPLF daga cikin jerin ƙungiyoyin ta’addancin ƙasar.

Hakan na zuwa ne watanni huɗu bayan da ƙungiyar ta sanya hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi da gwamnatin ƙasar.

Yarjejeniyar da aka cimma cikin watan Nuwamban bara a Afirka ta Kudu ta kawo ƙarshen rikicin da aka kwashe shekar biyu aka gwambzawa.

Cire sunan ƙungiyar TPLF daga jerin ƙungiyoyin ta’addanci na daga cikin yarjejeniyar, wadda ta ƙunshi mayar da muhimman ayyukan gwamnati zuwa yankin tigray da ke arewacin ƙasar.

To sai dai majalisar dokokin ƙasar ba ta cire sunan ƙungiyar ‘Oromo Liberation Army’ wadda a lokacin yaƙin ta bayyana mubaya’arta ga ƙungiyar TPLF.

Firaministan ƙasar Abiy Ahmed ya sha cewa a shirye yake wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma da ƙungiyar a Afirka ta Kudu.

Leave a Reply