EFCC ta mayar da dan takarar majalisar Kogi zuwa Legas.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta ce ta mayar da dan takarar majalisar dokokin jihar Kogi, Ismaila Atumeyi wanda aka kama a Abuja bisa zargin damfara a banki zuwa jihar Legas.

An kama ɗan siyasar, mai takara wakilcin mazabar Ankpa ll a majalisar dokokin jihar a karkashin jam’iyyar NNPP ne, a ranar Lahadin da ta gabata tare da wani Joshua Dominic, wanda ake zargi da damfara a wani samame da suka kai yankin Gwarinpa a babban birnin taraiya, Abuja.

Hukumar EFCC ta kama Atumeyi da karin wasu mutum biyu, Joshua Dominic da Abdulmalik Salau Femi, tsohon ma’aikacin banki, bisa zarginsu da yin kutse a ɓangaren bankin kasuwanci tare da damfarar hukumar sama da N1.4bn.

A ranar Talata ne kuma EFCC ta bayyana cewa ta kwato Naira miliyan 32 da dala $140,500 daga hannun Atumeyi yayin da ta kai samame a maboyar sa, inda aka kwato dala $470,000 daga hannun Abdulmalik a jihar Legas.

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce an dauke Atumeyi zuwa jihar Legas domin yi masa tambayoyi daga wata tawagar jami’an hukumar.

Leave a Reply