Hukumar yaki da hana cin hanci da rashawa ta kasa EFCC, ta bayyana shirinta na daukaka kara don kalubalantar hukuncin da wata babbar kotun tarraya dake zamanta a Abuja ta yanke na hana cigaba da shari’ar da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Abia Sanata mai ci mista Orji Ozo Kalu, wanda ake zargi da wawuren kudaden da suka haura naira biliyan 7 da miliyan daya.
EFFC ta cikin wata sanarwa data fitar tace Akwai kuskure a hukuncin da alkalin Kotun Inyang Ekwo ya yanke na rashin mutunta dokar kasa bisa la’akari da hukuncin baya bayan nan da kotun ta yanke na bada umarnin Dakar da cigaba da sauraron shari’ar.
Kotun dai takadar da hukumar ta EFFC daga cigaba da tuhumar Mista Kalu Sanata mai ci wanda a baya ya fuskanci hukuncin daurin shekaru 12 a gidan kaso sakamakon zarginsa da wawure naira biliyan 7 da miliyan 1 a sanda yake kan kujerar gwamna a jihar Abia.