Elon Musk ya kammala cinikin Twitter.

Fitaccen attajirin nan a duniya Elon Musk, ya kammala yarjejeniyar dala biliyan 44 domin siyan kamfanin Tuwita bayan watanni da aka shafe ana ce-ce-kuce.

Rahotanni sun ce shugaban kamfanin Parag Agrawal, na daga cikin manyan jami’an kamfanin da aka sallama daga aiki. Rahotanni sun ce mutane da dama za su yi matukar farin ciki da sallamar Prag Agrawal, Kuma wannna wata alama ce da Elan Musk, ke nunawa na cewa shi ne mai cikakken iko.

Daman an ji haushin yadda aka haramtawa tsohon shugaban Amurka Donald Trump, amfani da shafin na Tuwita.

Elon Musk, ya ce yana son ya sayi kamfanin na Tuwita ne saboda jama’a ba don ya yi kudi ba.

Wata yar jarida da ke aiki da jaridar Washington Post ta Amurka ta bayyana yadda za a samu sauye sauye bayan mr Musk ya mallaki kamfanin sada zumuntar na Tuwita.

Tace ina gani ya kamata a shirya dawowar Donald Trump, cikin masu amfani da wannan shafi.

 Yunkurin Elon Musk, na sayen shafin Tuwita ya janyo zazzafar muhawara kan makomar shafin – gwamnatin Amurka ma ta nuna damuwa kan tasirin da kafofin sada zumunta ke da shi.

Sai dai bukatar Musk ta sayen Tuwita kan $44bn ya ci gaba da jan hankali musamman kan tarihin irin wallafe-wallafe da hamshakin mai kudin yake yi.

Leave a Reply