Duniya na fuskantar barazanar ƙarancin ruwa – MDD

Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa duniya na cikin barazanar fuskantar ƙarancin ruwan sha saboda amfani da buƙatar ruwa sosai da ake da ita ga kuma matsalar sauyin yanayi.

“Duniya na cikin matsalar faɗa wa mawuyacin hali saboda yawan amfani da ruwa,” in ji rahoton.

Wallafa rahoton na zuwa ne gabanin taron MDD na farko kan ruwa tun 1977.

Dubban wakilai ne daga sassan duniya za su halarci taron kolin na kwanaki uku da za a yi a birnin New York daga yau Laraba.

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce yanayin da ake amfani da ruwa a yanzu ba mai ɗore wa ba ne, kuma wannan yanayin tamkar jinin bil Adama ne ke tsiyayewa saboda matsalolin ƙarancin ruwan da ɗumamar yanayi da gurɓatar muhalli ke ci gaba da haifarwa.

Babban editan da ya wallafa rahoton da aka kira da World Water Development Report wanda MDD ta kaddamar – Richard Connor – ya ce duniya na fuskantar gagarumar matsala.

“A halin yanzu, kashi 10 cikin 100 na al’umomin duniya na rayuwa ne a karkashin wani yanayi na matsanancin karancin ruwa. A cikin rahotonmu, mun ce kimanin mutum biliyan uku da miliyan 500 na rayuwa ne a karkashin rashin wadataccen ruwa na tsawon wata guda a kalla cikin kowacce shekara.”

Mista Connor ya faɗa wa manema labarai cewa ana ci gaba da samun matsala waje samar da ruwan sha a faɗin duniya.

“Idan bamu shawo kan matslar ba, zai iya zamantowa barazana a duniya,” in ji shi.

Jami’ar MDD wadda za ta karɓi bakuncin taron kan batun ruwa, Usha Rao Monari, ta faɗa wa BBC cewa ya kamata a san yadda ake kula da kuɗaɗe da aka tanadar na samar da ruwan sha a nan gaba.

“Akwai ruwa mai yawa a doron duniya, idan muka san yadda za mu kula da shi, to za mu iya zama tare da ruwa na gwamman shekaru masu zuwa,” in ji Monari.

“Ina ganin ya kamata gwamnatoci su samu sabbin hanyoyi samun kuɗaɗe, da sabbi hanyoyi na amfani da ruwan sha. Ina ganin fasaha da kuma kirkire-kirkire za su taimaka wajen ganin yadda za a kula da ɓangaren ruwa da kuma amfani da shi.”

Taron wanda gwamnatocin Tajikistan da Netherlands za su karɓi bakunci, zai tara mahalarta 6, 500, wanda ya kunshi ministoci 100 da kuma shugabannin gwamnatocin duniya daban-daban.

Leave a Reply