Dillalan man fetur kusan dubu 9 ke gab da rasa lasisin su a Najeriya

Akalla dillalan man fetur dubu 9 ne a Najeriya ke gab da rasa lasisin cinikayyar su a kasar sakamakon rashin sabunta su, adalilin kawo karshen wa’adin da kamfanin NNPC ya gindaya musu.

Yanzu haka dillalan ta hannun kungiyar su ta IPMAN ta gabatar da roko na musamman ga kamfanin NNPC da ya yiwa Allah wajen tsawaita wa’adin sabunta lasisin har zuwa karshen watan Yuli mai zuwa.

Dillalan sun kuma roki hukumar dake kula da lasisin a karkashin NNPC da ta gaggauta sakin lasisin da aka sabunta ga wadanda suka samu nasara.

Babban jami’in hulda da jama’a na kungiyar dillalan Chinedu Ukadike ya gabatar da wannan bukata a takardar da ya rabawa manema labarai. Yanzu haka ‘yan Najeriya na fuskantar matukar wahala wajen samun man fetur a gidajen mai saboda karancin sa, abinda ya haifar da dogayen layuka a biranen kasar tare da tsadar sa a kasuwannin bayan fage ko kuma hannun ‘yan bumburutu.

Leave a Reply