Dattijo Dan shekara 119 Mafi tsufa a Najeriya.

Idris Usman Al’hassan

Alaramma Alhaji Salisu Alhassan ‘Yan Turaki, shine dattijo mafi yawan shekaru a Najeriya.

An haife shine a wani kauye da ake kira ‘yanturaki dake mazabar Shifdawa ta karamar Bindawa a jihar Katsina a shekarar 1905. Yayi karatun Muhammadiyya wato karatun allo a kasar gabas, wacce a yanzu ake kira da birnin Maiduguri. Yayi aurensa na farko tun a zamanin Sarki Abdullahi Bayero, inda ya auri wata Mace mai suna Rabi’atul Badawiyya, wacce Allah ya albarkace su da ‘yaya 6, 4 mata biyu maza. Bayan ta rasu ne ya dauki wasu shekaru da dan dama kafin ya kara aure, saboda jin radadin mutuwar ta. Alhaji Salisu ‘Yan turaki ya rubuta Alqur’ani mai girma tun yana matashi, sannan ya rungumi harkar noma da kiwo ka’in da na’in, ta sanadin haka nema ya biya kudin kujerar aikin hajji a zamanin gwamnatin soji ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A hirarsa da Guarantee Radio, Alhaji Salisu ya bayyana cewa a baya yazo Kano sau da dama, lokacin da suke zuwa shi da wani amininsa su karbi zakka a wajen Attajirin dan kasuwar nan marigayi Alhaji Alhassan Dantata mahaifin Alhaji Aminu Dogo, lokacin Kano ma babu al’umma sosai, ba gidaje a unguwar Goron Dutse da wasu unguwannin cikin birni sai gidaje can daya can daya. Duk tarin wadannan shekaru na Alhaji Salisu ‘Yanturaki, har yanzu shine yake jan Sallah a masallacin kofar gidan sa, yana gani da idanunsa biyu, yana yin tafiyar kafa zuwa kauyukan dake kusa da inda yake zaune, sallar Juma’a bata wuce shi indai lafiyarsa kalau, kuma rikicin tsufa bai kama shi ba, ya kanje ko’ina ya dawo gida ba tare da batan hanya ba. Allah ya azurta Alhaji Salisu ‘Yan turaki da tarun ‘ya’ya da jikoki sama da dari uku 300 harma da tattaba kunne. Dattijon dai shine mafi tsufa da yawan shekaru a kasar mu Najeriya.

Leave a Reply