Dattawa a yankin Kano ta kudu sun bukaci Gwamnatin Jihar Kano data janye kudirinta na rusa masarautu.

Dattawan wadanda wakilcine na kananan hukumomi 16 dake yankin, sunyi wannan kirane yayin wani taron manema labarai da suka Kira.
Shugaban tawagar dattawan Alh Musa Salihu Doguwa, yace samar da masarautun Rano, Gaya, da Karaye bawai alfarma akayi musu ba la’akari da tsohon tarihin da masarautun ke dashi.
Musa Salihu yace, bayaga wancen tarihi, dawo da masarautun ya taimakawa al’ummar yankin wajen samun cigaba da karuwar arziki.

Alh Musa Salihu ya godewa ‘Yan Majalisar dokokin kano masu wakiltar Gaya da Takai da Doguwa da kuma Tudun Wada bisa goyon bayan da suka nuna akan masarautun.
A makon daya gabata ne dai Majalisar dokokin jihar kano ta rushe dokar data samar da Karin masarautu hudu a kano bayaga masarautar kano abinda yakaiga adadin masarautu a jihar kano zuwa biyar.

Leave a Reply