Kwamitin bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaƙi da rashawa a Najeriya ya yi zargin cewa kusan duk ɓangarorin gwamnati a dukkan matakai, ba sa ba da haɗin kan da ya kamata wajen yaƙi da matsalar cin hanci a ƙasar.
Kwamitin ya ce hatta jam’iyyar APC mai mulki wadda ta sa yaƙi da cin hancin cikin alkawurranta a lokacin neman zaɓe ba ta taka rawar da ta dace ba ta wannan fuskar.
Sakataren kwamitin, Farfesa Sadik Isah Raɗɗa ne ya bayyana haka a wata hira da Sashen Hausa na BBC kan inda aka kwana a yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.
Farfesa Sadik Isa Radda ya ce faɗa da rashawa ba aikin mutum guda ba ne ko shugaban kasa shi kadai, amma sai ya kasance hatta jam’iyyarsa ta zura ido ba ta taka rawar gani.
Ya ce akwai rawar da ya kamata a ce fanoni da dama sun taka kama daga na tsaro da hukumomi da gwamnoni da sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki.
Sannan ya ce ya kamata yaki da rashawa ya kasance akidar APC tunda jami’iyyar ta kawo mutane da dama daga matakai daban-daban mulki.
Farfesa Sadik ya ce faɗan ba na mutum guda be ne, tunda tasirin matsalolin rashawa kowa na girba ba wai kawai abin na shafar shugaban kasa da iyalansa ba ne, ko su kadai za a zurrawa ido su yaƙi rashawar ba.
‘Jam’iyyar ba shugaban kasa da mataimakinsa kadai ta kawo mulki ba ta kawo ‘yan majalisa da ciyamomi, kwamishinoni da gwamnoni da ma’aikata daban-daban da ya kamata a ce suna bada gudunmawa wajen gyaran kasa.
“Ina iya kau da kai idan PDP taƙi yaƙar rashawa tunda dama ba ta ce za ta yaƙi rashawa ba, amma APC babu zance kawar da kai”
‘Haɗin-kai’
Ya ce duk da cewa a karkashin PDP aka kafa hukumar yaƙar rashawa ba wani aiki suka yi a wancan lokacin ba.
A cewar Farfesa Sadik gwamnatin wancan zamanin ce ta kafa hukumar domin farautar wasu mutane na daban domin ribarta ta hanyar kai farmaki.
Farfesa ya ce ba ribar shugaba Buhari ko mataimakinsa kadai ba ne, abu ne da ya shafi kowa da kowa na kasa.
Ya ce EFCC, ICPC da NFIU da sauran hukumomin yakar rashawa na ayyukansu su mikawa shugaban kasa, sai dai ba aikinsa ba ne ya rinka katsalanda ko umartar a kama mutane.
Farfesa Sadik dai na ganin akwai gagarumar rawa ko wanne ɗan kasa zai taka wajen hada kai a marawa gwmanati ta kawar da rashawa a Najeriya.
Rahoton Cislac
Waɗanan bayanai daga kwamitin bai wa shugaban Najeriya shawara kan rashawa na zuwa ne makonni bayan wani rahoto da aka fitar kan cin hanci da rashawa.
Ƙungiyar CISLAC ce ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Transparency International (TI) suka fitar da rahoton da ke cewa har yanzu babu wani sauyi da aka samu a Najeriya game da yaƙi da cin hanci da rashawa.
Kungiyoyi daban-daban ne suka tattara bayanai kan matsalar cin hancin a duniya, inda TI ta saka Najeriya a matsayi na 154 cikin ƙasashe 180 a shekarar 2021.
Sabon rahoton ya ce Najeriya ta samu maki 24 ne kacal daga cikin 100 da ya kamata a ce ƙasa ta samu don tsira daga matsalar rashawa.
Matsalar ta kara ƙazancewa a Najeriya ne idan aka kwatanta da alƙalumman shekarar 2020, inda ta samu maki 23 cikin 100.
Martanin Buhari
Sai dai shugaban Muhammadu Buhari ya ce babu kamshin gaskiya a rahoton da ƙungiyar Transparency ta fitar da ke cewa kasarsa ce ta biyu da ta fi cin hanci da rashawa a Afirka ta Yamma.
Shugaban ya ce ba a yi musu adalci ba a rahotan, domin duk wanda ya san ƙasar da abubuwan da ke faruwa ya san gwamnatinsu na kokari matuka.
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari dai a ko da yaushe na bayyana fifiko da rawar gani a fanin rashawa wanda ke cikin alkawuranta tun yakin neman zabe.