Dalibai Miliyan 1.4 Da Suka Rubuta Jarra-bawar UTME Sun Ci Maki Kasa Da 200

Sakamakon da hukumar shirya jarabawar sharar fagen shiga manyan makarantu a kasar nan (JAMB), ya nuna cewa dalibai 1,402,490 daga cikin 1,842,464 sun gaza samun maki 200 daga cikin maki 400 na jarabawar.

Adadin daliban da suka kasa cin sakamakon sun dauki kaso 78 cikin dari na duka daliban da suka zauna domin rubuta jarabawar kamar yadda sakamakon da JAMB ta fitar ya nuna.

Da yake bayar da bayani kan sakamakon jarabawar daliban shugaban hukumar, Farfesa Ishak Oloyede, ya ce, hukumar ba ta saba wallafa sunayen wadanda suka yi zarra a jarabawar ba, illa iyaka tana fito da jerin yadda sakamakon ya kaya.

Oloyede ya kuma ce an rike sakamakon jarabawar dalibai 64,624, inda ake kan gudanar da bincike kan zargin satan amsa, sahihancin cibiyar zana jarabawar su da dai sauransu.

Leave a Reply