Dala ce ta haddasa tsadar man fetur a Lagos da Abuja – IPMAN

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta kasa IPMAN ta dora alhakin karancin man da ake fama das hi a Legas da Abuja da sauran jihohin kasar kan tsadar farashin Dala da kuma yadda Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya gaza sakin wadataccen man.

Akwai dogayen layukan ababen hawa a sassan Lagos da Abuja duk da cewa, ana sayar da lita guda akan farashin Naira 180 ko ma fiye da haka, matsalar da ta tilasta wa direbobin motocin haya tsauwala kudin mota ga fasinjoji.

Jami’in Hulda da Jama’a na Kungiyar IPMAN, Chief Ukadike Chinedu ya ce, manyan jiragen ruwa na shigo da man fetur cikin kasar nan ta kan iyakar Legas, yayin da kananan jiragen ruwa ke kai man zuwa tashoshin jiragen ruwa na Legas da Warri da Fatakwal da dai sauransu.

Jami’in ya bayyana cewa, mawuyaci ne masu gidajen man su sayar da shi akan Naira 145 kowacce lita a daidai lokacin da farashin hayan jirgin ruwan ya karu daga Dala dubu 38 zuwa Dala dubu 108.

Leave a Reply