Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka ‘yan fashin daji 4 a Kaduna

Dakarun sojojin Najeriya masu take Opretion sharar daji sunyi luguden wuta a maboyar ‘yan fashin daji dake kusa da Tsohon Gayan, a yankin karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar

Yace a yayin farmakin sojojin sun kuma kama bindiga kirar AK47 da ma’ajiyar harasashi guda daya da alburusai 22 da babur guda daya.

Leave a Reply