Dakarun Eritrea na ficewa daga yankin Tigray

Ana ci gaba da janye dakarun Eritrean waɗanda suka kwashe shekara biyu suna taya sojojin Habasha yaƙi a yankin Tigray, zuwa wasu yankuna da ke kusa da kan iyaka.

Wani mazunin garin Shire a yankin na Tigray ya shaida wa BBC cewa sun ga manyan motoci ɗauke da dakarun sojin na Eritrea daga wasu yankunan birnin Axum suna tsallakawa zuwa garin Sheraro da ke kusa da kan iyaka.

Haka kuma wasu mazauna garin sun faɗa cewa a ‘yan kwanankin nan suna yawamn ganin motoci maƙare da dakarun na ficewa daga yankin.

Kawo yanzu dai ba a sani ba ko wannan matakin alama ce ta janye sojojin daga yankin ne.

An yi ta samun kiraye-kirayen ficewar dakarun na Eritrea daga yankin, yayin da ake ci gaba da sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Habasha da yankin na Tigray.

Leave a Reply