Cristiano zai koma Sporting Lisbon a watan janairu

Cristiano ronaldo kan iya barin kungiyarsa ta Manchester domin komawa tsohuwar kungiyasa ta Sporting Lisbon a watan janairu, dan wasan mai shekaru 37
yana fuskantar mawuyacin hali a kakar wasan bana wanda a iya cewa wannan shine karon farko da yashiga irin wannan hali na rashin kokari a tsawon shekaru sama da ashririn yana fafata wasa a manyan gasuka.

cristiano dai ya dawo kungiyar ta manchester united ne a karo na biyu bayan yabar kungiyar a karshen kakar wasannin ta 2009 inda ya koma Real Madrid, ana
rade-radin dai Manchester United din na kokarin maye gurbinsa da dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen.

Leave a Reply