Coronavirus a Kano: Mutum 576 suka kamu, 21 suka rasa rayukansu

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano a Najeriya ta ce ya zuwa daren Asabar, an samu karin mutum 29 da suka kamu da cutar korona a jihar.

Hakan na nufin adadin mutanen da ke dauke da cutar a Kano ya kai 576, tun bayan bullar cutar a jihar, sai dai kuma an sallami mutum 32, inda 21 suka rasu.

Jadawalin jihohin da cutar ta bulla da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC ta fitar ya nuna Kano ce ta biyu a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 1,764 da Abuja babban birnin kasar inda ake da mutane 343.

A ranar 11 ga watan Afrilu ne hukumomi a Kano suka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar kuma tun daga wannan lokacin aka rika samun karuwar mutanen da annobar ta shafa, kuma ci gaba da gwaje-gwaje a jihar bayan an sami tsaiko ya sa aka samu karuwar yawan wadanda ke dauke da cutar.