Ministan kwadago da nagartar aiki Dr Chris Ngige, ya roki kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU da ta kawo karshen yajin aikin da take yi na tsawon wata guda kafin cikar wa’adin da suka dauka.
Rohotanni sun bayyana cewa Ngige wanda yayi ganawar sirri ta tsawon awanni da shugabannin kungiyar ta ASUU ministan ya kalubalanci kungiyar ta ASUU kan zarin da suka yiwa gwamnatin na rashin mutunta yarjejeniyar da suka cimma a tsakaninsu.
Ngige a hirarsa da manaima labarai yace gwamanti na yin duba kan bukatan da kungiyar ta ASUU ta gabatar, yana mai cewa zaiyi wata ganawa da kungiyar da shugabannin addinai a mako mai kamawa.
Kazalika shugaban kungiyar malaman jami’o’in ta kasa ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke yayin zantawarsa da manaima labarai ya jadadda matsayar kungiyar na kin janye yajin aikin da suka tsindima matukar ba’a cika musu bukatunsu ba