China ta ci tarar wata kungiyar barkwanci $2m kan yin raha ga sojojin ƙasar

China ta ci tarar kamfanin barkwanci $2m kan yin raha ga sojojin ƙasar.

Hukumomin ƙasar sun ce abin da kamfanin barkwancin mai suna Shanghai Xiaoguo Culture ya yi ba abu ne mai kyau ba.

Sun ce wani daga cikin mai yi a kamfanin barkwanci, Li Haoshi, ya kwatanta sojojin ƙasar da karnuka a cikin wata rawa da ya taka.

Kamfanin ya amsa laifin da ya aikata da kuma tarar da aka sanya masa, inda kuma ta sallami Li Haoshi daga aiki.

Leave a Reply