China ta ba Amurka zaɓi na zaman lafiya ko zaman gaba tsakaninsu

Ministan harkokin wajen China, Wang Yi ya ce alaka tsakanin kasarsa da Amurka ta fara daidaituwa a ‘yan watannin nan, amma kuma wasu abubuwa da ke haifar da sabani tsakaninsu na karuwa.

Mista Wang ya ce zabi ne tsakanin hada kai na kasa da kasa ko kuma gabar da za ta iya kaiwa ga babban rikici.

Ministan harkokin wajen na China yayi wannan jawabi ne a yayin bude tattaunawar da suke yi da takwaransa na Amurka Antony Blinken, a Beijin, a ziyarar da Mista Blinken ke yi a Chinar.

Mista Wang, wanda ya ce dangantaka wadda take tamkar ta doya ta manja tsakanin manyan kasashen biyu, ta fara daidaituwa a watannin nan, amma kuma wasu abubuwa da ke kara haddasa sabani a tsakaninsu na ci gaba da karuwa.

A don haka ya ce zabi ya rage na ko dai su hada kai a tsakanininsu ko kuma a ci gaba da gaba da fito na fito da ka iya kaiwa ga dauki-ba-dadi.

Leave a Reply