Ce-ce-ku-ce ya barke tsakanin jaridar Thisday da Tinubu

Ce-ce-ku-ce ya barke tsakanin kamfanin Jaridar Thisday da darakatocin yakin neman zaben dan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Ahmad Tinubu.

Jaridar ta Thisday ta zargi daraktan yada labaran kwamitin yakin neman zaben Tinubu, Bayo Onanuga, da na tsare-tsare da kula da harkokin sadarwa Dele Alake da yunkurin rufe bakin ‘yan jarida.

Thisday ta ce yunkurin da daraktocin yakin neman zaben na Tinubu ke yi ba shi da maraba da tsarin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na take hakkin fadar albarkacin bakin ‘yan jarida.

Sai dai kwamitin yakin neman zaben na Tinubu, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana zargin na mai jaridar ta Thisday a matsayin wanda “ba shi da tushe ballantana makama.”

Kwamitin yakin neman zaben na Tinubu ya ce babu wata kafar yada labarai da suka ware don su ci zarafinta.

Haka kuma ya zargi jaridar ta Thisday da yada wasu kasidu ta hanyar amfani da kalaman cin fuska da zagi ga dan takarar jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan ya nuna rashin kwarewarsu karara.

Leave a Reply