CBN ya musanta katse hanyoyin aika kuɗi ta intanet
A dai-dai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da fuskantar ƙalubale wajen aika kuɗi ta intanet da kuma amfani da na’urar cirar kuɗi ta POS, babban bankin kasar – CBN ya musanta bayanan da ake yada wa cewar ya bayar da umurnin katse hanyoyin tura kuɗi ta intanet a lokacin zaben da za a yi a karshen mako.
Labarin ƙaryar ya jefa fargaba a zukatan ƴan ƙasar har ta kai mutane sun fara rige-rigen zuwa kasuwanni domin tanadar abubuwan buƙata kamar abinci da man fetur domin ajiye su a gida har zuwa lokacin zaɓe da kuma bayansa.
Labarin ƙaryar da ya karaɗe ko ina musamman a manhajar Whatsapp.
A ranar Laraba ne dai CBN ya fito ya ƙaryata rahotannin da ake ta yaɗawa ba tare da yin ƙarin haske kan batun.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, CBN din ya ce babu gaskiya a labarin katse intanet kuma ba daga wurinsa sanarwar ta fito ba.
Batun sauya takardun kuɗi a Najeriya ya janyo cece-kuce a ɓangarori da dama tun bayan fara aiwatar da tsarin a Disambar 2022.